Zan kawo canjin gaskiya a Katsina inji Sanata Zaharadden Babba Mazoji

23
HON. ZAHARADDEN BABBA MAZOJI
HON. ZAHARADDEN BABBA MAZOJI
HON. ZAHARADDEN BABBA MAZOJI
HON. ZAHARADDEN BABBA MAZOJI

Dan takarar Sanatan shiyyar Funtu a jahar Katsina,  karkashin inuwar jam’iyar PDP yanci, a shekara ta 2019 Hon. Zaharadden Babba Mazoji, ya yi alkawarin kawo canjin gaskiya idan al’umma su ka zabe shi, tare da shan alwashin cewa, zai inganta rayuwar matasa da mata, da yunkurin samar da aikin yi da inganta sha’anin lafiya, da kuma gabatar da kudurori da za su kawo cigaba.

A wata ganawa da wakilin Hago Radio, Zahadden Mazoji, ya kara da cewa,  manufofin ba za su tabbata ba har sai al’ummar shiyyar Funtuwa, sun ba da hadin kai, wajen daukar sabuwar tafiyar matasa, wanda a cewarsa yana daya daga cikin masu bukatar kawo cigaban.

Mazoji, ya ce, ya fito siyasa ba da nufin cin mutuncin wani ko wata ba, inda ya cigaba da cewa, wajen Allah ya ke nema, idan yasamu ko ya rasa ya gode masa.

Leave a Reply