Zan gyara Ungogo da Minjibir —-Hon Sani Ma’aruf

43
HON SANI MA'ARUF
HON SANI MA'ARUF

 

Daga Kabiru Inuwa

HON SANI MA'ARUF
HON SANI MA’ARUF

Dan takarar majalisar tarayya na kananan hukumomin Ungogo da Minjibir a shekara 2019 karkashin inuwar jam’iyar APC tsagin Gandujiyya, Hon Sani Ma’aruf, wanda ya ke rike da matsayin shugaban kasuwar abinci ta Afrika, ya ce zai kawo gyara domin kyauta al’ummar yankin idan su ka zabe shi.

Hon Sani Ma’aruf, ya fadi haka ne a wata ziyara da ya kai tashar Hago Radio, wanda ya ce muddin ya kai matakin nasara zai kawo sabon fasalin jagoranci.

“Ina so in gayawa Hago Radio cewa, muddin kananan hukumomin Ungogo da Minjibir, idan su ka lamince da ni a matsayin wakilin su a majalisar tarayya karkashin inuwar jam’iyar APC tsagin Gandujiyya, zan kawo sauyi domin cigaban jama’a.

Kazalika, Hon Sani, ya jinjinawa gwamna Ganduje kan yadda ya ke samar da shugabanci na gaskiya da rikon amana.

Leave a Reply