zan cigaba da yin Fallasa–Sanata Isah Misau

72
SANATA ISA HAMMA MISAU
SANATA ISA HAMMA MISAU
SANATA ISA HAMMA MISAU

Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya Isa Hamma Misau, ya ce, taimakawa al’umma da kare muradan su,  su ne kashin bayan fitowarsa takarar sanata.

Sanatan, ya fadi haka ne a wata ganawa da wakilin Hago Radio, a birnin tarayya Abuja, inda ya ce, tuni ya shirya wajen sadaukar da rayuwarsa a kowanne hali domin kare mutuncin jama’ar da ya ke wakilta.

“Kamar yadda ka sani wakilcin mutanen Bauchi ta tsakiya su ka zabo ni, don haka, ba ni da shakka ko tsoro dare ko rana, a shirye na ke da sadaukar da rayuwata don kare mutuncin mutane na, saboda haka, ina ba su tabbacin cewa, ba gudu baja da baya,idan mun ga cuwa-cuwa ko murdiya za mu tona, domin kawo gyara,

ina nan kamar yadda a ka sanni wajen fallasa duk abin da ba gaskiya”

Leave a Reply