Zan cigaba da bijiro da ayyukan raya kasa—Hon Sale Marke

42
HON SALE AHMED MARKE
HON SALE AHMED MARKE
HON SALE AHMED MARKE
HON SALE AHMED MARKE

Dan majalisar dokokin jahar Kano mai wakiltar karamar hukumar Dawakin Tofa Hon Sale Ahmed Marke, ya ce zai cigaba da samar da ayyukan raya kasa domin ganin yankinsa ya zama abin alfahari.

Dan majalisar, ya yi wannan alkawari ne lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, inda ya ce yana alfahari da mutanensa, bisa ba shi dama har karo uku yana jagorancinsu.

“Ya zama wajibi in yi alfahari da mutanen karamar hukumar Dawakin Tofa, domin sau uku su na zabe na a majalisar dokokin Kano,d omin yi mu su wakilci, bashakka ina ba su tabbacin cewa, kowacce rana ina nan wajen zakulo hanyoyin cigaba, an kuma gani a kasa, da irin ayyukan da na samar”

Marke, ya kuma roki mutanen Kano, su sake zabar gwamna Ganduje a karo na biyu.

Leave a Reply