Zamfarawa sun yi namadar zaben jam’iyar APC in ji Zamfara youth mobilazation

30
JAHAR ZAMFARA
JAHAR ZAMFARA
JAHAR ZAMFARA
JAHAR ZAMFARA

Wata kungiyar matasan jahar Zamfara, masu fafutikar  wayar da kan jama’a, wato Zamfara Youth mobilazation, sun yi tir da zaben jam’iyar APC a matkina jahar, saboda gaza kare  musu dukiya da rayukan jama’a.

Shugaban kungiyar Kwamared Umar Gusau, shi ne ya furta haka a yayin wani taron karawa juna sani da kungiyar ta shirya, domin wayar da kan matasan jahar Zamfara, kan zaben Dr, Bello Matawallen Maradun, a matsayin gwamnan jahar karkashin jam’iyar PDP a shekara ta 2019.

Shugaban kungiyar ya kara da cewa ” lokaci ya wuce da za su sake zabar APC a jahar Zamfara, saboda ba za ta iya kawo cigaba, tun da sun gwada sun gani, donhaka,  ya ce ya zama wajibi matasa su yi karatun nitsu domin zaben Dr Bello Matawalle, duba tarihinsa na samar da cigaba, da temakon jama’a a ” cewar shugaban kungiyar.

Leave a Reply