Zaben Kano akwai ‘yan matsaloli— Abubakar Abdullahi Dan garin nan

48
KWAMARED ABDULLAHI DAN GARIN NAN
KWAMARED ABDULLAHI DAN GARIN NAN
KWAMARED ABDULLAHI DAN GARIN NAN
KWAMARED ABDULLAHI DAN GARIN NAN

Wani dan fafutikar kare hakin bil’adama Kwamared Abubakar Abdullahi Dangarin nan, ya ce, zaben kananan hukumomi da aka kammala kwanan nan akwai ‘yan matsaloli, da su ka kunshi rashin kai kayan aiki kan kari a wasu wurare, da kuma zargin da ake yi na ba yara damar yin zabe.

Dangarin nan, ya nuna takaicinsa kan abubuwan da su ka faru, inda ya yi kira ga shugaban hukumar zaben ya nemi afuwar mutanen Kano, kan abin da ya faru.

“An gudanar da zabe a jahar Kano, amma mu na bukatar shugaban hukumar zaben ya nemi afuwar mutanen Kano, saboda rashin kai kayan aiki wasu wuraren kan lokaci”

Zaben dai, mutane da yawa na kokawa saboda rashin tsari da kuma mulkin mallaka.

Leave a Reply