Za a tsige mataimakin shugaban kasar Zimbabwe

63
SHUGABA MUGABE
SHUGABA MUGABE

Shugaban  kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya fara yunkurin tsige mataimakinsa Emmerson Mnangagwa, daga kujerar mulki, wata majiya  ta shaidawa HagoRadio cewa, wannan yunkuri ya biyo bayan yadda magoya bayan mataimakin , su ka kunya ta matar shugaban kasar a wani taron gangamin siyasa, tare da yi mata ihu.

A cikin jawabin shugaban kasa Mugabe;  ya ce “Mnangagwa yana da damar shiga ko’ina da magoya  baya da kafa  jam’iyyar siyasa”.

Rahotanni sun  ce, shugaban kasar ya nuna rashin jin dadinsa a fili, inda ya bukaci mataimakin nasa da magoya baya da su ringa yi masa biyayya ko kuma ya kore su daga mukamin.

 

Leave a Reply