Yar Jarida Salamatu Sabo Bakin Zuwo ta yi wani abin fada

68
HAJIYA SALAMATU SABO
HAJIYA SALAMATU SABO

 

DAGA KABIRU INUWA HAYINHAGO

An bukaci masu aikin jarida su yi koyi da  Hajiya Salamatu Sabo Bakin Zuwo, shugabar sashin shirin siyasa ta gidan Rediyon Express da ke Kano, daya daga cikin sojojin baka Hon Ado Yalo mai tibi, shi ne ya yi wannan roko a wata ganawa da Hago Radio.

Mai Tibi,  ya bayyana Hajiya Salamatu Sabo, a matsayin gogaggiyar ‘yar jarida mai aiki tukuru da gaskiya, ya kuma sake bayyana ta a matsayin karima mai karrama mutane yara da manya, wanda a cewarsa ya zama wajibi muddin a na bukatar cigaban kasa ‘yan jaridu su yi ko yi da halin ta.

“Ina so in gaya maka Kabiru Inuwa Hayinhago, Hajiya Salamatu jarima ce a fagen aikin ta, kuma mai gaskiya da kaunar jama’a, wadda ta ke yin aikin ta ba nuna bambanci, donhaka, na ke rokon wannan gidan rediyo naku zai yi ko yi da halayen ta domin  samun cigaba cikin sauri”

Leave a Reply