Yan ta’adda sun hallaka mutane masu yawa a jahar Kaduna

24
WASU 'YAN TA'ADDA
WASU 'YAN TA'ADDA
WASU 'YAN TA'ADDA
WASU ‘YAN TA’ADDA

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun hallaka mutane shida a daren jiya Laraba, a kauyen  Kaguru da ke karamar hukumar Birnin-Gwari a jahar Kaduna.

Majiyar Hago Radio ta ce, shigar maharan cikin kauyen ke da wuya, su ka fara barin wuta, lamarin da mutane su ka fara fitow daga gidajensu domin ganin abin da ke faruwa, inda su ka yi amfani da wannan dama waje  bude  mu su wuta.

Wani mazaunin garin ya ce, bayan sun tarwatsa mutanen sai su ka shiga cikin garin, tare da yin awon gaba da shanun da ke daure cikin daji.

“Bayan sun bude wutar, sai su ka shiga cikin gari inda su ka yi awon gaba da shanun cikin daji, harwayau, sun sakawa wasu gidajen wuta.

 

Leave a Reply