‘Yan majalisar Zambia za su tsige shugaban kasar

10
Shugaban kasar Zambia
Shugaban kasar Zambia
Shugaban kasar Zambia
Shugaban kasar Zambia

Wakilan jam’iyyar hamayya a kasar Zambia, sun fara gudanar da wani shirin  yin kudurin doka a zauren majalisar, domin  tsige shugaban kasar Edgar Lungu.

Rahotanni da su ka iske Hago Radio, ya ce tuni kusan kashi uku cikin hudu na ‘yan majalisar, karkashin jam’iyyar United Party for National Development  sun rattaba  hannu kan kudurin dokar, wanda aka gabatar a  jiya juma’a  a gaban majalisar

Cikin mutanen da suka sanya hannu kan kudurin, sun hada da tsofaffin ministoci Chishimba Kambwili, da Harry Kalaba, wadanda  su ka kasance mambobin jam’iyya mai mulki.

 Daukar matakin, ya biyo bayan yadda ‘Yan majalisar su ka  ce, shugaban kasar bai  iya aiki ba, sai kuma cin hanci da suke zarginsa

 

Leave a Reply