‘Yan bindiga dadi sun sace shugaban ‘yansanda

78
Yansanda a bakin aiki
Yansanda a bakin aiki
Yansanda a bakin aiki
Yansanda a bakin aiki

Wasu ‘yan bindiga dadi sun  yi awon gaba da wani baturen ‘yansanda Amos Ali,  mai kula da shiyyar sarkin pawa, a karamar hukumar Munya da ke jahar Neja, tare da wasu mutane biyar ciki har da  dogarinsa.

Majiyar Hago Radio, ta ba mu labarin cewa, hadarin ya faru ne lokacin da su ke kan hanyar dawowa daga Minna zuwa Sarkin Pawa. Wata majiya daga iyalan baturen ‘yansandan ta ce, masu garkuwar, sun nemi kudin fansa naira miliyan sha shida.

Gabannin dauke Baturen ‘yansandan, an ce maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da harsashi ya hallaka wani dan kasuwa da ke kusa da wajen.

Hago Radio, ta tuntubi kakakin hukumar rundunar yansandan jahar Neja Adewale Babalola, amma har lokacin hada wannan  labari su na wata ganawa ta masu ruwa da tsaki

Leave a Reply