wasu yan fashi da makami sun bindige wani jigo a jam’iyar PDP

72
YAN BINDIGA DADI
YAN BINDIGA DADI
YAN BINDIGA DADI

A safiyar yau juma’a Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, sun bindige wasu mutane biyar a jahar Zamfara, ciki har da wani fitaccen  jigo a jam’iyar PDP mai suna Alh Sa’idu, garkuwan ‘yan ware.

Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne lokacin da ‘yan fashin su ka tare motar da mutanen ke ciki, kan hanyar Funua zuwa Gusau, tare da bude musu wuta, lamarin da hakan ya janyo mutuwar su.

Wani mazaunin garin Gusau Alh. Sa’idu Mai shanu, ya gayawa majiyar Hago Radio cewa, an harbi Alh. Sa’idu ne a wuya, lokacin da su ka budewa motar wuta.

Majiyar Hago Radio, ta yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun hukumar rundunar ‘yan sandan jahar Zamfara, amma ba ta samu jin ta bakin sa ba.

 

Leave a Reply