Wasu Likitoci za su yi dashen kan mutum

45
DASHEN KAI
DASHEN KAI
DASHEN KAI
DASHEN KAI

Wasu gungun likitoci  a kasar chana karkashin jagorancin Farfesa Sergio Canavero,za su gudanar da  wani aikin dashen kan mutum  wanda shine na farko a tarihin likitanci.  Dashen kan wanda zai  dauki tsawon awanni goma sha takwas, za a  gudanar da shi ne kan  wasu gawarwakin mutane guda biyu.

Wakilin HagoRadio na sashin kiwon lafiya Abba Tofa, ya ce  Dashen kan, za a  fara gudanarwa  kan wani dan sa kai mai fama da cutar mutuwar barin jiki, wanda zai ba da damar taimakawa mutanen da ke fama  cutittika
Amma  kwararru a  kasar Birtaniya  ta bakin Dr. James Fildes, na sashin dashen sassan jikin Dan’adam na asibitin koyarwa na Jamiar South Manchester,  yace  Dashen kan da Farfesa . Canavero, ya ke shirin  gudanarwa ba komai ba ne face rashin da’a da kuma aikata babban laifi.

Leave a Reply