Wani mutum ya nemi a daure dansa shekaru ashirin a kurkukun Kano

74

Wani mutum mai suna Malam Sulaiman, mazaunin garin Kalekun Kanawa da ke yankin karamar hukumar Dawakin Tofa  Arewacin Kano da ke Najeriya, ya gabatar da korafi ga  ‘yansandan garin Dawaki, ya na neman su garkame dansa mai suna Muhammadu, ko kuma su mika shi kurku tsawon shekaru ashirin, domin a cewar sa yana tsoron cigaba da zama  da shi, sakamakon yunkurin  hallaka shi.

Hago Radio, ta bakin wakilin ta Abduljalal Adam, ta jiyo  mahaifin matashin na cewa, ba zai iya zama da dan nasa ba,  saboda ya zama annobar zamani,  aikinsa  rigima da sace-sacen kayan mutane, wanda a cewarsa  ya tsiya ta shi.

“Na  kai kara wajen ‘yansandan  garin Dawaki, ina so su dauke min wannan yaro Muhammadu, duk da kasancewar ni na haife shi, amma ya fi karfi na, ya zama barawo, ga shaye-shaye, kullun  cewa ya ke wallahi baba ni ne ajalin ka, sai na kashe ka”

Za mu kawo mu ku  cigaban labarin, domin sauraren hira kai tsaye da wannan mahaifi sai ka shiga HAGO RADIO INTERNATIONAL. A manhajjar Tunein.

 

Leave a Reply