Wani dan majalisar tarayya zai aje mukaminsa

37
HON ABUBAKAR CHIKA
HON ABUBAKAR CHIKA
HON ABUBAKAR CHIKA
HON ABUBAKAR CHIKA

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Shiroro/Rafi/Munya daga jahar Neja Hon. Abubakar Chika, ya ce zai aje neman matsayin cigaba da zama dan majalisar tarayya a shekara ta 2019, saboda lalacewar lamura da kuma neman azirta kai a dare daya na wasu shugabanni.

Cikin wata takarda  da dan majalisar ya aikewa shugabannin jam’iyar APC na jahar Neja, ya ce hakika akwai bukatar shugabanni su gyara halayensu, ya kuma ce ya dauki matakin ne domin haka musulunci ya yi tanaji.

” Mu a koyarwar musulunci duk wanda ya ce a zabe shi to yakamata jama’a su yi watsi da shi, domin be cancanta ba, donhaka 2019 ba zan sake tsayawa takara ba, sai idan al’umma sun bukata.

Leave a Reply