Talakawan Najeriya su ne mafi shan wahala a Duniya ko kun san dalili?

29
WASU 'YAN NAJERIYA KE NAN
WASU 'YAN NAJERIYA KE NAN
WASU 'YAN NAJERIYA KE NAN
WASU ‘YAN NAJERIYA KE NAN

Binciken wata kungiyar sa’ido da ganin kwakwaf  ta kasar Amurika, ta fitar da wani rahoton sirri wanda ya fallasa  yadda talakawan Najeriya  su ka zama sahun baya na fuskantar matsin rayuwa a fadin Duniya, duk da yawan arziki da kasar  ke da shi.

Masanan sun bayyana Najeriya, a matsayin kasa mai daraja duba da albrkatun kasa da dunbin mutane da ta kunsa,  sai dai a cewar kungiyar, rashawa da cin hancin  wasu daga cikin shugabannin kasar ya hana ta motsawa bare talakawan kasar su amfana. Harwayau, kungiyar, ta bayyana rashin aikin yi a matsayin wata hanyar dirkushewar cigaban kasar, wanda ta kara da cewa,  idan mahukuntan kasar, su ka cigaba da barin talakawan  batare da samar mu su da makoma ba, nan da lokaci kadan za su iya yin bore domin kwatar yanci.

Dadindadawa, kungiyar ta nuna takaicin ta, yadda talakawan Najeriya ke fama da rashin tsarin kiwon lafiya, da yawan mabarata, musamman a yankin Arewa, wanda ta danganta hakan da sakacin hukumomin kasar.

Leave a Reply