Sule Lamido ya zama dan takarar PDP a shugaban Kasa

73
Tsohon Gwamna Lamido
Tsohon Gwamna Lamido

Tsohon Gwamna LamidoTsohon gwamnan jahar Jigawa DR. Sule Lamido, ya aikewa shugabannin jam’iyar PDP na jahohin Najeriya wata rubutacciyar wasika, inda ya bayyana musu kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa a shekara ta 2019.

Cikin wasikar, Sule Lamido, ya ce har yanzu Najeriya na mafarkin cigaba ne, amma a cewarsa idan aka bashi amana zai iya gyara kasar, tare da samar da ayyukan cigaba.

“Yau kimanin shekaru 57 da samun ‘yancin kan Najeriya, amma har yanzu ana mafarkin cigaba ne kawai, amma mudin na samu nasara zan gyara kasar don tabbatar da tsari irin na kyawawan shugabanin baya masu adalci”

Sule Lamido, ya kara da cewa, ko shakka babu, jam’iyar PDP za ta iya kafa mulkin kasa, sakamakon ayyukan raya kasa da jam’iyar ta gudanar a baya.

Leave a Reply