Shugaban majalisar dokokin jahar katsina ya yi wani abin fada

45
Rt. Hon. Abubakar Yahaya Kusada
Rt. Hon. Abubakar Yahaya Kusada

Daga Kabiru Inuwa

Rt. Hon. Abubakar Yahaya Kusada
Rt. Hon. Abubakar Yahaya Kusada

Shugaban majalisar dokokin jahar Katsina Rt. Hon Abubakar Yahaya Kusada, ya jinjinawa al’ummar mazabarsa ta karamar hukumar Kusada, bisa hadin kai da goyon baya da su ke ba shi wajen sauke nauyin jagorancin da su ka dora masa.

Shugaban majalisar ya ce ya na matukar jin dadi kwarai da gaske da yadda su ke nuna masa halin karamci da kyutayi, a ziyar mako-mako da ya ke yi a mazabarsa domin ganawa da su, wanda a cewar sa  kowanne shugaba abin tambaya ne a gobe kiyama.

‘Ina so in gaya maka duk da kasancewa ta shugaban majalisar dokokin jahar Katsina, duk sati idan ba wani aiki ya sha kai na ba, ina kai ziyara mazaba ta domin ganawa da kuma jin matsaloli, idan da dan abin bayarwa in bayar, idan kuma babu in ba da hakuri rayuwa ce, amma ni ban yarda jam’ar da su ka zabe ni ba in guje su, ko in tsere, wannan haramun ne a tsari na, kuma ina so in gaya maka duk wani shugaba abin tambaya ne a gobe kiyama, don haka,wajibi ne na yi kokari wajen ganin na kwatanta adalci”

Hago Radio ta gano cewa, shugaban majalisar dokokin jahar Katsina, ya kasance  mutum na farko mai matsayi irin nasa, da ya ke kai ziyara duk sati ga mazabarsa.

Leave a Reply