Rigima ta barke tsakanin shugaban hukumar tara kudaden jahar Kano- Sani Dambo

106
Hukumar tara kudin Kano

Hukumar tara kudin Kano

Rigima ta barke tsakanin shugaban hukumar tara kudaden shiga na jahar Kano, Sani Abdulkadir Dambo, da wani matashi mai suna Bashir Dandalama, daga yankin karamar hukumar Dawakin Tofa.

Shugaban hukumar dai, ya zargi matashin da cin zarafinsa da kuma bata masa suna, tare da mai girma gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a wata kafar watsa labarai ta radiyo mai matsakaicin zango na FM.

Binciken Hago Radio, ya gano cewa, matashin ya furta wasu kalmomi ne na nuna rashin gamsuwa da kamun ludayin shugaban hukumar Sani Dambo, “hakika gwamna yana bukatar ya kawo gyara a masu rike da mukaman siyasa na Dawakin Tofa, domin ba sa taimakonsa” a cewar kalaman Bashir Dandalama.

Wannan kadan kenan cikin kalmomin da matashin ya yi, tare da kama sunayen wasu daga ciki, wanda ya kunshi sunan shugaban hukumar tara kudaden, harma da sunan kani ga mai girma gwamnan.

Yanzu haka dai, wancan matashi bayan kwashe kwana guda a ofishin hukumar ‘yansanda na karamar hukumar Dawakin Tofa, tuni an arce da shi babbar hedikwatar yansanda domin cigaba da bincike.

A nasa bangaren shugaban hukumar tara kudaden jahar Kano Sani Dambo, ya gayawa Hago Radio cewa “Ni ba abin da zan ce kan wannan labari, domin Bashir Dandalama, ya ci mutunci na tare da mai girma gwamna, don haka, magana ce ta cikin gida, ba ma bukatar  wasu a Duniya su san abin da ya faru”

Hukumar tara kudin Kano

 

Leave a Reply