Ranar Asabar 28-10 Fadar Sarkin Gombe za ta yi mamaki

77
Ango Musa da Amarya Rukayya

Ranar Asabar 28 ga watan Oktoba, fadar mai martaba sarkin Gombe, za ta karbi bakunci daruruwan al’umma daga ko ina a fadin Najeriya, domin halartar wani gagarumin bukin wasu manyan masoya da su ka zo da sabon salo a fagen kauna.

Wakilin Hago Radio, na jahar Gombe, Gidado Umar Kumo, ya ba mu labarin cewa daurin auren zai kasance ne tsakanin Alh Musa Habibu, {Musa Bushasha] da amaryarsa Rukayya Dahiru, a cewarsa za a daura auren a masallacin Buba Yero, da ke fadar sarkin Gombe, da misalin karfe 11 na safe.

Cikin mutanen da ake tsammanin zuwansu akwai dan takarar gwamnan APC Muhammadu Inuwa, da kuma manyan baki.

 

 

 

 

Leave a Reply