Najeriya ta fada hannun gidadawa-inji tsohon gwamna Sule Lamido

25
Tsohon Gwamna Lamido
Tsohon Gwamna Lamido
Tsohon Gwamna Lamido
Tsohon Gwamna Lamido

Tsohon gwamnan jahar Jigawa, kuma dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jam’iyar PDP Alhaji Sule Lamido, ya ce  mulkin Najeriya ya fada hannun gidadawa marasa kishi bare manufar kishin kasa. Ya fadi haka ne a jiya a garin Calabar.

Cikin jawabinsa Lamido, ya kara da cewa, jam’iyar APC mai mulki, ta kasa kawo manufofin ciyar da kasa gaba, har yanzu tana tafiya a tsohon tsarin da jam’iyar PDP ta yi watsi da shi shekara da shekaru.

Ya kara da cewa, a baya an zargi mulkin PDP da kashe tiriliyan 6 cikin shekaru 16 wajen gudanar da ayyukan raya kasa, sai gashi cikin shekaru uku na jam’iyar APC ta kashe tiriliyan 20, wanda ya ce yana mamakin ta yadda makauniya adawa ta ke hana wasu mutane fadar gaskiya.

Leave a Reply