Mutanen jahar Adamawa za su koma Kamaru

44
Mutanen Madagali
Mutanen Madagali
Mutanen Madagali
Mutanen Madagali

Sakamakon yawaitar  hallaka rayuka da ‘yan kungiyar Boko Haram ke yi a karamar hukumar Madagili da ke jahar Adamawa, al’ummar yankin sun fara yunkurin gudun hijira zuwa kasar Kamaru domin samun mafaka.

Wani shugaban al’ummar yankin  mai suna malam Umar, shi ne ya fadi haka a yau Alhamis, lokacin da su ke karbar kayan tallafi daga hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA, biyo bayan wani mummunan hari da aka kai musu cikin wannan sati.

Sanata  mai wakiltar yankin Binta Garba, ta nuna rashin jin dadin ta da faruwar lamarin, inda ta ce sansanin na ‘yan Boko Harambe fi tazarar kilo mita uku da garin Madagali ba, sai dai ta ce za ta gabatar da matsalar wajen gwamnatin tarayya don daukar mataki. 

 

 

 

Leave a Reply