Matan aure sun zama ‘yan kwaya a jahar Yobe–Sarkin Tikau

28
Mugayen kwayoyi
Mugayen kwayoyi

Daga Yusif Sa’ad

Mugayen kwayoyi

Sarkin Tikau  Alhaji Muhammad Abubakar Ibn Grema,   ya nuna rashin jin dadinsa sakamakon karuwar  shan mugayen kwayoyi tsakanin matan aure, a yankin masauratarsa da ke karamar hukumar  Nangere  a jahar Yobe.

Sarkin ya bayyana haka ne a Lahadin nan, cikin fadarsa da ke  Sabon Garin Nangere, in da ya ce, hakika shaye-shayen ya na   rusa kyawawan dabi’oi da  janyo mutuwar aure da gurbacewar zuri’a 

“,Gaskiya masaruta ta, tana cikin rudani domin shaye-shaye ya zama ruwan dare ga matan aure da matasa, wanda su ke amfani da Wiwi,Tramol, Kodin da sauran su, abin takaici an wayi gari cikin kasuwa wasu mutane marasa kishin kasa, su na sayar da kayan maye a fili batare da tsoron hukuma ba, ina ganin addu’a ita ce maganin wannan masifa da annoba”

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply