Mata 110 sun gurfana gaban kwamishinar matan Kano

45
http://www.hagoradiointernational.com/wp-content/uploads/2017/11/Kwamishinar-mata-Yardada-Bichi-
Ciyaman Musa Sa’ad

 A yau juma’a, Karamar hukumar Dawakin Tofa a arewacin jahar Kano karkashin jagorancin Malam Musa Sa’ad, ya jagoranci kaddamar da rabon tallafin kudade naira dubu goma goma ga mata guda 110  wadanda su ka fito daga mazabu sha daya na karamar hukumar.

Cikin jawabinsa shugaban karamar hukumar Malam Musa Sa’ad, ya godewa gwamnan jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, na ba su damar bayar da tallafin kudaden,  inda ya yi fatan matan da su ka amfana za su yi aiki da kudaden don yin sana’o masu dorewa. Harwayau, ya kuma ba da tabbacinsa ga sauran al’ummar karamar hukumar, inda ya ce su na nan su na tanaji na kawo tsare-tsare masu amfani don kyautata rayuwar jama’a.

A nata jawabin kwamishinar mata ta jahar Kano, Hajiya ‘Yardada Bichi, ta roki matan da su ka amfana su tabbatar sun yi sana’oin da su ka samu horo a kansu.

“Ina fata matan da za ku karbi wadannan kudade ku yi sana’oin da ku ka samu horo a kansu, domin da sannu wadannan kudade za su burunkasa”

Leave a Reply