Malaman Addinai suna da hannu a rashawa—-Obasanjo

61
Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo
Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo
Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya zargi shugabannin addinai da fifita manyan jami’an  gwamnati da ake zarginsu da halatta kudin haram da kuma ruf-da-ciki da dukiyar al’umma.

Obasanjo, ya kara da cewa lokaci yayi da ‘yan najeriya za su tashi tsaye wajen yaki da fifita manyan jami’an gwamnati da ake zargi da almundahana da dukiyar al’ummar Kasar.

Tsohon Shugaban Kasar, ya bayyana hakan ne, a lokacin da ake gudanar da wata lacca mai taken “Yaki da cin hanci da kalubalan da matasan nahiyar Afrika ke fuskanta” wanda aka gudanar a Birnin Ibadan dake Jahar Oyo. Inda ya kara da cewa, ya kamata a rinka kallon wadanda suka yi wakaci-watashi da dukiyar al’umma a matsayin mahandama kuma marasa kishin al’umma.  

 

 

Leave a Reply