Leburori ‘Yan Arewa na fuskantar matsala a jahar Osun

36
Masu hakan Zinare
Masu hakan Zinare

Leburori ‘yan Arewa masu hakan  zinare  a yankin karamar hukumar Ilesa a jahar Osun, sun fara fuskantar matsin lamba , na biyan harajin ba gaira ba dalili har naira dari biyu kowacce rana, kudin dai na a matsayin kudaden cin  arzikin kasa da suke yi.

Daya daga cikin masu hakan zinaran dan asalin jahar Kano, Muhammad

Masu hakan Zinare
Masu hakan Zinare

Bello Gitsu=Gitsu, ya gayawa majiyar mu cewa,su na cikin tsaka mai wuya, wanda hakan ya ke barazanar raba su da aikin saboda biyan harajin kowacce rana, wanda a cewarsa mutum zai iya kwashe kwana talatin ya na neman zinaran bai samu ba.

“Babu shakka muna cikin matsin lamba, domin a yanzu leburori masu hakan zinare an dora mana harajin biyan dari biyu kowacce rana walau mun samu nasarar hakowa ko ba mu samu ba,  ina gaya maka wani lokacin mutum zai iya kwashe wata daya cif bai hako ba, don haka mu na   bukatar shugaban kasa ya kawo mana agaji”

Leave a Reply