Tuesday, August 7, 2018
Gida Blog
Daga Abba Tofa   Matemaki na musamman ga shugaban karamar hukumar Tofa Rufa'i Wangara, ya ce ko shakka babu, masu cewa Hon Jobe, ta bare 2019 akwai karancin fahimta a tare da su, donhaka ya bukace su  su sauya tunani tun da wuri. Da ya ke ganawa da wakilin Hago Radio Abba Tofa, ya kara da cewa siyasa ta ba kowa damar...
Eng Hamisu Abubkar Lambu
Daga Amadu Salisu Bachirawa Dan takarar majalisar tarayya mai neman wakiltar kananan hukumomin Dawakin Tofa Rimingado da Tofa, Hon. Eng Hamisu Abubakar Lambu, ya jinjinawa dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dawakin Tofa, Hon Sale Ahmed Marke, da dan majalisar jaha mai wakiltar kananan hukumomin Tofa da Rimingado, Hon. Muhammed Bello Butubutu, inda ya ce, shugabanni ne abin koyi, masu...
Hon Mustafa Yusif
Dan majalisar jaha mai wakiltar karamar hukumar Jibiya, a zauren majalisar Katsina, Hon Mustafa Yusif, ya samu yabo ta bakin jama'arsa, kan ayyukan raya kasa da ya samar, wanda a cewarsu, shekaru da dama ba su taba samun jagaora kamar sa ba. Daya daga al'ummar yankin Bishir Umar, shi ne ya fadi haka a wata ganawa da wakilin Hago Radio...
Shugaban kasar Zambia
Wakilan jam'iyyar hamayya a kasar Zambia, sun fara gudanar da wani shirin  yin kudurin doka a zauren majalisar, domin  tsige shugaban kasar Edgar Lungu. Rahotanni da su ka iske Hago Radio, ya ce tuni kusan kashi uku cikin hudu na 'yan majalisar, karkashin jam'iyyar United Party for National Development  sun rattaba  hannu kan kudurin dokar, wanda aka gabatar a  jiya...
Eng Hamisu Abubkar Lambu
Dan takarar majalisar tarayya a kananan hukumomin Dawakin Tofa Rimingado da Tofa,  karkashin inuwar  jam'iyar APC, Eng Hamisu Abubakar Lambu, ya yi alkawarin magance fatara da rashin aikin yi, idan al'umma su ka zabe shi. A wata ganawa da Hago Radio, Eng Hamisu, ya ce bashakka, idan ya samu nasara zai kafa kwamitoci na lafiya da ilimi, da kwamitin samar...
Mahamoud Tofa
Dan takarar majalisar tarayya a yankin Dawakin Tofa Rimingado da Tofa a jahar Kano,  karkashin jam'iyar APC Hon Mahamoud Tofa, ya nuna takaicinsa da yadda ya ke yin kukan zuci idan ya ga shugabanni sun yi watsi da mutanen da su ka zabe su, wanda  ya ce abin takaici ne kuma  abin mamaki. A wata  ganawa da manema labarai, Mahamoud...
Wani dan kasuwar abinci ta Afrika da ke Dawanau Alh Auwalu Yusif, Dawakin Tofa, mai  fafutikar ganin cigaban  gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sake nanata kudirin cewa, ya zama wajibi duk mai kishin kasa, ya jinjinawa gwamnatin Ganduje, kan yadda ya hana jahar Kano, rushewa duk da matsalar kudi da Najeriya ke fama. Alh Auwalu, ya kara da...
ALH_AUWALU_YUSIF
Wani dan kasuwa mai zaman kansa, a kasuwar abinci ta Afrika dake Dawanau Alh Auwalu Yusif, Dawakin Tofa, ya ce ko shakka babu gwamnan jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, zai sake maimaitawa duba da ayyukan raya kasa da ya ke samarwa a jahar Kano. Alh Auwalu Yusif, ya fadi haka ne a ofishinsa a yau Asabar, a wata ganawa...
Eng Abubakar Kabir Bichi
Shugaban kamfanin gine-gine na BICO Construction Nig Limited, Eng. Abubakar Kabir Bichi, ya gwangwaje wasu daga cikin dalibai karamar hukumar Bichi, su dari biyu  da kudade domin biyan jarabawar NECO. Cikin jawabin mai temaka masa kan harkokin yada labaran zamani Abdullahi Maisudan, ya ce, taimakon ya zama wajibi duba da yadda daliban su ka hadu da matsalar jarabawar, wanda yanayin...
MARYAM SANDA DA 'YAR TA
Maryam Sanda, wadda wata kotu a birnin tarayya Abuja, ke tuhuma da laifin kashe mijinta, ta shirya wani gagarumin taro domin taya 'yar ta murnar bikin ranar zagowar haihuwarta.  Wannan lamari ya faru ne kwana daya da yin belin ta, kamar yadda alkalin kotun Yusif Halliru, ya amince, saboda samun rahoton rashin  lafiyar da ta ke fama, sakamakon ciki...