kimanin matasa dubu biyar za su aje tafiyar Gandujiyya saboda hana Dr. Nafi’u mukami

24
Dr. Nafi'u Yakubu
Dr. Nafi'u Yakubu
Dr. Nafi'u Yakubu
Dr. Nafi’u Yakubu

Kimanin matasa dubu biyar a yankin karamar hukumar Tofa, da ke jahar Kano, za su aje tafiyar Gandujiyya, domin nuna takaicinsu dangane kin  nada Dr. Nafi’u Yakubu Muhammad Dan Nono, a mukamin da gwmamna Ganduje, ya yi masa alkawari wata da watanni,   a cewar matasan, sau uku ana yi masa alkawarin mukami, amma a karshe sai a dauka a ba wani, donhaka, su ka ce, wannan shi ne  lokaci na karshe da su ka yanke shawarar barin tafiyar Gandujiyya.

Shugaban matasa mai jagorantar wannan tafiya Bala Umar, ya ce sun dauki matakin batare da sanin Dr. Nafi’u ba,  amma dai ganin yadda ya zama kurar baya, da yadda gwamna Ganduje, har yanzu ya yi watsi da mukamin da aka yi masa alkawari, saboda haka, su ka dauki wannan mataki na barin tafiyar Gandujiyya.

“Kamar yadda kowa ya sani Dr. Nafi’u, jagora ne abin fahari, mai tausayin mara lafiya da kudi ko babu, wannan tasa lokacin da mu ka ji gwamna Ganduje, zai ba shi mukami mun yi godiya, amma har yanzu shiru, mun kuma tuna a baya an yi masa irin wannan, wanda a karshe aka hana shi mukamin, tunda yanzu ma, mun ji shiru, to shi ma gwamnan yakamata, ya ji shiru, mun hada kungiyar matasa sama da dubu biyar za mu aje tafiyar Gandujiyya”

Leave a Reply