Katin Whot, ya sa an hallaka wani matashi a Zamfara

46
WUKA DA JINI
WUKA DA JINI
WUKA DA JINI
WUKA DA JINI

Wani matashi  mai suna Anas, ya hallaka abokinsa ta hanyar daba masa wuka, a Unguwar Dallatu da ke birnin Gusau.

Wani wanda abin ya faru akan idonsa mai suna Abubakar Abubakar, ya gayawa majiyar HagoRadio cewa, matashin ya hadu da abokin nasa lokacin da ya ke gudanar da wasan katin Whot inda ya bukaci a bashi katin.

“Al’amarin ya faru ne lokacin da matashin mai suna Anas, ya zo ya iske abokinsa yana wasan katin Whot,  sai ya bukaci a ba shi katin, amma ya ce ba zai bayar ba donhaka, ya zaro wata wuka ya na cewa zai kashe shi, nan take mutanen da ke wajen su ka tare shi, sabodahaka, ya tafi kamar ya hakura, amma daga baya ya sake dawowa ya daga wukar ya daba masa a kirji. Yana kokarin guduwa wasu sojoji da ‘yansanda da su ka zo wucewa su ka damke shi”

Yanzu haka dai, wancan matashi  yana hannun jami’an tsaro don girbar abin da ya shuka.

 

 

 

Leave a Reply