Kano ta kusa samun canjin gaskiya–A A Zaura

59
ABDULSALAM ABDULKARIM A A ZAURA
ABDULSALAM ABDULKARIM A A ZAURA
ABDULSALAM ABDULKARIM A A ZAURA
ABDULSALAM ABDULKARIM A A ZAURA

Dan takarar gwamnan jahar Kano karkashin inuwar jam’iyar GPN mai alamar hannu Alhaji Abdulsalam Abdulkarim A A Zaura, ya nanata kudirinsa na samar da cigaba mai dorewa a jahar Kano, muddin ya samu nasarar zama gwamnan jahar.

Wannan jawabi ya fito ne lokacin wata ganawa da wakilin HagoRadio, inda ya ce jahar Kano a kwai fuskoki da dama wanda an barta a baya, kasancewar ta babbar giwa a Najeriya.

” Kamar yadda na sha fadawa mutane cewa, jahar Kano uwa ce a Najeriya, amma ta wasu fuskokin an barta a baya, amma dai ina da tabbacin cewa ba don nafi wani ba, idan mutanen jahar Kano su ka  zabe ni kamar yadda su ka kira ni na amsa kira zan kawo gyara da sabbin tsare-tsare, musamman ingata ilimi da harkokin lafiya da samarwa matasa d aikin yi musamman wadanda su ka kammala karatu”

Kazalika, A A Zaura, ya yi kira ga magoya bayansa da kasancewa masu yin siyasa cikin mutunci da kaunar juna.

Leave a Reply