Jahar Zamfara ta shiga tsaka mai wuya–Bello Muhammed Matawallen Muradun

25
BELLO MUHAMMED
BELLO MUHAMMED
BELLO MUHAMMED
BELLO MUHAMMED

Tsohon dan takarar gwamnan jahar Zamfara na jam’iyar PDP Alhaji Bello Matawallen Muradun, ya nuna takaicinsa a fili kan abin da ya kira halin matsi da kuncin rayuwa, da shugabannin jahar Zamfara su ka jefa mutanen da su ke jagoranta.

A wata ganawa da wakilin Hago Radio, Matawalle ya ce, mutanen jahar Zamfara  na cikin halin matsi sakamakon rashin tsaro da su ke fama, da  kisan kai da kwashe dukiyoyin su, Inda ya kara da cewa, abin takaici ne kan yadda mahukuntar jahar su ka yi watsi da al’amarin.

“Ina cikin cikin halin takaici kan yadda  aka jefa mutanen Zamfara, cikin halin rashin tsaro da kuma hallaka su ba ji ba gani, kuma abin mamaki jagororin jahar sun yi watsi batare da daukar wani matakin magance matsalar ba”

Harwayau, Bello Matawalle, ya jajantawa mutanen Zamfara, kan yadda a shekara ta 2015 su ka yi watsi da cancanta su ka  dauki masu ci da addini.

” Ina jajantawa mutanen Zamfara kan yadda masu ci da addini su ka yaudare su, yanzu kuma su ka jefa su cikin matsala ta rashin tsaro da kisan mutane, wanda a baya an ce PDP ce ke yin kisa, yanzu kuma fa?

Leave a Reply