Ina yin kukan zuci idan na shugaba ba ya kishin jama’arsa inji Hon Mahamoud Tofa

17
Mahamoud Tofa
Mahamoud Tofa
Mahamoud Tofa
Mahamoud Tofa

Dan takarar majalisar tarayya a yankin Dawakin Tofa Rimingado da Tofa a jahar Kano,  karkashin jam’iyar APC Hon Mahamoud Tofa, ya nuna takaicinsa da yadda ya ke yin kukan zuci idan ya ga shugabanni sun yi watsi da mutanen da su ka zabe su, wanda  ya ce abin takaici ne kuma  abin mamaki.

A wata  ganawa da manema labarai, Mahamoud Tofa, ya yi alkawarin cewa, mudin al’umma su ka zabe shi ya yi alkawarin yin jagoranci na gaskiya, musamman harkar lafiya ilimi da bayar da horon sana’oi da  da jari.  Harwayau, ya kara da cewa nan ba da jimawa ba, zai bayar da jari ga matan kananan hukumomin DawakinTofa, Rimingado da Tofa, da gyara  tuka-tuka, da kuma daukar nauyin yara karatu a cikin gida, da  tura dalibai shida kasashen waje domin koyo karatun likitanci.

Leave a Reply