Idan ba Hon Tijjani Jobe APC ta gama yawo a jahar Kano–Rufa’i Wangaram

15
HON TIJJANI ABDULKADIR JOBE

Daga Abba Tofa

 

HON TIJJANI ABDULKADIR JOBE

Matemaki na musamman ga shugaban karamar hukumar Tofa Rufa’i Wangara, ya ce ko shakka babu, masu cewa Hon Jobe, ta bare 2019 akwai karancin fahimta a tare da su, donhaka ya bukace su  su sauya tunani tun da wuri.

Da ya ke ganawa da wakilin Hago Radio Abba Tofa, ya kara da cewa siyasa ta ba kowa damar yin ra’ayinsa, amma cin fuska da keta haddin mai gidansa Hon Jobe, da wasu matasa su ka dauka ta hanyar juya hotonsa, su na cewa 2019 ta bare rashin aikin yi ne da karancin tunani.

” Ina so in ja hankalin abokan tafiyar siyasa ta matasa, kan wani bakin tsari na rashin da’a da wasu daga ciki su dauka, wato, tsarin Jobe ta bare, to su sani sun makaro, domin idan ba irin su Jobe, a siyasar APC a Kano ta gama yawo, duba da yadda yake temakon matasa da sauran al’umma”

Leave a Reply