Ibrahim Yaro ya ja kallo a masallacin Juma’a

58
IBRAHIM YARO DAWAKIN TOFA
IBRAHIM YARO DAWAKIN TOFA
IBRAHIM YARO DAWAKIN TOFA
IBRAHIM YARO DAWAKIN TOFA

Yau Asabar, daruruwan mutane sun yi dafifi a masallacin juma’a na wajen Dawakin Tofa, inda su ka shaida daurin auren wasu zaratan masoya da su ka dauki dogon lokaci su na yin soyayya, wato Hafizu Muhd Yaro, da amaryarsa Salma Umar.

Wakilin HagoRadio, Abba Badamasi, ya ce al’umma daga ko’ina sun amsa kiran uban ango Ibrahim Yaro, wanda ya ke tsohon hannu a fagen aikin jarida.

A wata ganawa da a kai da  Ibrahim Yaro, ya godewa mutanen da su ka amsa kira, kazalika ya yi rokon addu’a daga mutane domin samun dorewar zaman lafiya tsakanin angwaye da amare. ” Hakika mutane sun amsa kira, mu na godiya Allah ya bar zumunci, ina fatan kowa ya koma gida lafiya”

 

Leave a Reply