Ibrahim Shekarau ya zama dan takarar shugaban kasa a PDP

70
Malam Ibrahim Shekarau
Malam Ibrahim Shekarau
Malam Ibrahim Shekarau

Tsohon gwamnan jahar Kano Dr. Malam Ibrahim Shekarau, ya aikawa masu ruwa da tsaki na jam’iyar PDP kudirinsa na yin takarar shugabancin kasa a shekara ta 2o19.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan Sule Ya’u Sule, shi ne ya tabbatarwa manema labarai haka, inda ya ce kafin ya mika bukatar ya tuntubi al’umma da dama.

Cikin wasikar da ya aikewa wani makusancinsa Hasan Indabawa, mai dauke da kwanan watan  22 ga watan Ogusta 2017, Malam Shekarau ya ce tun shekara ta 2015, al’umma su ka bukaci ya sake fitowa takarar shugabancin kasa, amma sai a wannan lokaci ya ga dacewar amsa kiran domin kyautatawa al’umma.

Leave a Reply