Hukumar WAEC ta rike sakamakon jarabawar dalibai

40
MINISTAN ILIMI ADAMU ADAMU
MINISTAN ILIMI ADAMU ADAMU
MINISTAN ILIMI ADAMU ADAMU
MINISTAN ILIMI ADAMU ADAMU

Hukumar shirya jarabawar Afrika ta yamma WAEC, ta rike sakamakon jarabawar  daliban Najeriya na makarantu masu zaman kansu, har dubu sha hudu da dari bakwai da sittin da shida, 14,766. sakamakon magudin jarabawa.

Shugaban hukumar Olu Adenipekin, shine ya gayawa manema labarai ciki har da majiyar HagoRadio, cewa daukar matakin ya zama wajibi ganin yadda daliban su ka saki jiki wajen cin makauniyar kasuwa na shirya magudi.  Sai dai ya ce nan ba da jimawa ba, hukumar za ta mika lamarin ga kwamitoci na musamman da hukumar ta kafa, domin daukar matakin da ya dace.

Leave a Reply