Gwamna Masari shi ne abin koyi na—-Hon.Amiru Tukur

57
Hon Amiru Tukur
Hon Amiru Tukur
Hon Amiru Tukur
Hon Amiru Tukur

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Bakori da Danja Hon. Amiru Tukur, ya nuna godiyarsa ga gwaman jahar katsina Aminu Bello Masari, bisa namijin kwazon kyautata rayuwar katsinawa, inda ya ce, tsawon shekarun da ya kwashe bayan dawowar harkokin dimukaradiya, babu wani gwamna da ya taimaki jahar katsina sama da gwamna Masari.

Harwayau, Hon. Amiru, ya bayyana cewa, a harkokin jagoranci gwamna Masari shi ne abin koyinsa ” Ina so in tabbatar maka cewa,  gwamna Masari, ya kawo gyaran da ya dara kowanne gwamna a jahar Katsina, wani abin mamaki mutum ne mai karamci da hakuri ga rashin girman kai,  ni kai na, wani lokacin ina yin mamaki domin ba zan iya abubuwan da ya ke yi ba”

Hon. Amiru, ya kuma roki mutanen jahar Katsina su ci gaba da goyawa gwamnatin Malam Aminu Bello Masari, goyon baya, domin samun cigaba mai dorewa

 

Leave a Reply