Gandujiyya ta fi karfin kwankwasiyya–Hon Lawan Shehu Bichi

95
Hon Lawan Shehu
Hon Lawan Shehu
Hon Lawan Shehu
Hon Lawan Shehu

Tsohon dan majalisar tarayya na karamar hukumar Bichi Hon Lawan Shehu Garkuwan limamai, kuma majidadin sharifai na kasa, ya ce duba da ayyukan raya kasa na gwamnan jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya zama wajibi a rufa masa baya domin sake maimaita mulki a karo na biyu.

Hon. Lawan Shehu, ya kara da cewa, ya zama wajibi Kanawa musamman matasa su kaucewa tsarin tafiyar bankaura, ta hanyar rungumar tafiyar Gandujiyya domin ita ce tsari mai dorewa.

“Ina so in gaya maka cewa  Tafiyar Gandujiyya ta dau sahu a jahar Kano, duba da ayyukan da mai girma gwamna Ganduje, ya ke samarwa a jahar Kano, batun ma a ce akwai wani tsari bayan nasa magana ce mara tushe”

A karshe ya roki mutanen kano su cigaba da yin addu’oin samun zaman lafiya.

Leave a Reply