Ganduje zai sake maimaitawa inji Alh Auwalu Yusif

20
ALH_AUWALU_YUSIF

ALH_AUWALU_YUSIFWani dan kasuwa mai zaman kansa, a kasuwar abinci ta Afrika dake Dawanau Alh Auwalu Yusif, Dawakin Tofa, ya ce ko shakka babu gwamnan jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, zai sake maimaitawa duba da ayyukan raya kasa da ya ke samarwa a jahar Kano.

Alh Auwalu Yusif, ya fadi haka ne a ofishinsa a yau Asabar, a wata ganawa da manema labarai, inda ya ce, duba da ayyukan raya kasa da gwamna Ganduje, ya ke samarwa yakamata mutane su cigaba da rifa masa baya, musamman tattalin arziki da ake fama, amma ayyukan da ya samar sun fi karfin lissafi.

Harwayau, ya kara  godewa, dan majalisar dokokin jahar Kano Hon. Sale Marke, da shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Ado Tambai, da Yusif Bashiri da Ahmad Abas, wanda a cewarsa abokan tafiyar samar da cigaban gwamnatin Ganduje ne.

Daga bisani, Alh Auwalu, ya sake mika makamanciyar jinjina da godiya ga dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin Tofa, Rimingado da Tofa, Hon. Tijani Abdulkadir Jobe, kan  yunkurinsa na samar da ayyukan cigaba.

 

Leave a Reply