Ganduje zai nada Dr, Nafi’u Tofa, shugaban hukumar tara kudaden kiwon lafiyar Kano

29
Dr. Nafi'u Yakubu
Dr. Nafi'u Yakubu
Dr. Nafi'u Yakubu
Dr. Nafi’u Yakubu

Gwamnan jahar Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje, zai nada shugaban Asibitin Imam Wali Dr, Nafi’u Yakubu Muhammad Tofa, a matsayin shugaban sabuwar hukumar tara kudaden kiwon lafiyar ma’aikata ta jahar Kano.

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya, majalisar dokokin jahar Kano ta amince da hukumar, a matsayin kafa ta  adashin gata  ga ma’aikata, domin yankar wasu ‘yan kudade cikin albashinsu duk wata,  ita ma gwamnatin jaha za ta ringa ware  kaso mai tsoka daga harajin cikin gida da aka samu, domin sakawa a  hukumar da nufin inganta kiwon lafiya.

Wata majiya daga fadar gwamnatin Kano da zauran majalisar dokokin jahar, ta bayyana cewa, nan da kwanaki kadan zai karbi takardar kama aiki.

Mutane da dama, sun yi farin ciki tare da godewa gwamna Ganduje, bisa nada Dr, Nafi’u Tofa, a matsayin shugaban hukumar, dogaro da kwarewarsa da kuma nuna goyon bayan gwamnatin a ko yaushe.

Har ya zuwa yanzu dai, Dr Nafi’u shi ne shugaban Asibitin Imam Wali da ke Kano

 

Leave a Reply