Ganduje ya zama likitan Kanawa—Dr Nafi’u Yakubu Tofa

30
Dr. Nafi'u Yakubu
Dr. Nafi'u Yakubu

Daga Kabiru Inuwa Hayinhago

Dr. Nafi'u YakubuWani likitan gwamnati Dr  Nafi’u Yakubu  Dan Nono Tofa, ya jinjinawa gwamnan jahar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, kan kokarin bunkasa harkokin  kiwon lafiya,  musamman samar da asibitocin Giginyu da Zoo Road,  wanda  ya ce za su temaka wajen kawo karshen yawo kasashen ketare da nufin neman lafiya.

DR Nafi’u, ya kara da cewa bashakka gwamna Ganduje, ya kasance dan kishin kasa da kyautata kiwon lafiya, wanda a cewarsa ya zama wajibi kanawa su cigaba da rufa masa baya domin cimma bukatarsa.

A karshe Dr, Nafi’u, ya godewa kwamishinan lafiya na jahar Kano, Dr, Kabir Getso, da shugaban hukumar gudanarwar asibitocin jahar Dr  Aminu Ibrahim Tsanyawa,, bisa namijin kokarin su wajen bunkasa lafiyar jama’a.

Leave a Reply