Ganduje ya zama fitilar Kanawa–Hon Garba Yahaya Labour

42
HON GARBA YAHAYA LABOUR
HON GARBA YAHAYA LABOUR
HON GARBA YAHAYA LABOUR
HON GARBA YAHAYA LABOUR

Shugaban Kamsilolin karamar hukumar Dawakin TOfa da ke jihar Kano Hon. Garaba Yahaya Labour, ya ce gwamannan jahar Kano Dr. Abdullalhi Umar Ganduje, ya zama fitilar Kanawa, duba da ayyukan raya kasa da ya ke aiwatarwa duk da matsalar tattalin arzikin da kasar ke fama.

Ya yi wannan jawabi ne cikin wani sakon fatan alkairi da ya aikewa ga HagoRadio, ta hannun mai temakawa shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, kan yada labarai a kafofin sadarwar zamani Abdullahi ISaq Bataye, Inda ya ce sun yi farin cikin samar da  gidan Rediyon domin ya zo a lokacin da ake bukata wanda za su yi amfani da shi wajen yada manufofin gwamantin Ganduje, domin shaidawa Duniya ayyukan cigaba da su ke samarwa a jahar Kano.

Hon. Garba Yahaya, a karshe ya yi fatan HagoRadio za ta yi amfani da kwarewarta wajen bayar da sahihan labaran gasakiya.

Leave a Reply