Farfesa Muktar Atiku Kurawa sun daura zare da Kwalejin Polytecnic Kano

39
KWALEJIN ILIMI TA POLY
KWALEJIN ILIMI TA POLY
KWALEJIN ILIMI TA POLY
KWALEJIN ILIMI TA POLY

Shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta Polytechinc Kano, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, ya ja zaren damben samar da cigaba  mai dorewa ga malaman makarantar da sauran ma’aikata, tare da yunkurin shayar da daliban jahar Kano ilimi mai kwari, domin zama abin alfahari a fadin Duniya.

Tsohon shugaban sashin koyar da aikin jarida a matakin farko na makarantar, Malam Umar Faruk, shi ne ya yi wannan jawabi a yau Talata, yayin wata ganawa da wakilin Hago Radio a Ofishin magatakardar makarantar.

Cikin jawabinsa, Malam Umar ya kara da cewa, koshakka babu shugaban makarantar Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, jagora ne abin alfahari, ganin yadda cikin karamin lokaci ya  samar da cigaba, da kawo sabbin tsare-tsare.

A karshe Malam Umar, ya yi fata tare da rokon daliban makarantar za su dukufa wajen yi wa shugaban makarantar addu’a saboda samar da cigaba mai dorewa.

Leave a Reply