Eng Abubakar Kabir ya dauki matakin gyara zaman daliban Bichi a kan NECO

54
Eng Abubakar Kabir Bichi
Eng Abubakar Kabir Bichi
HUKUMAR NECO
HUKUMAR NECO

Babban hadimin gwamna Dr. Abdullahi Ganduje, kuma shugaban kamfanin gine-gine na BICO Eng. Abubakar Kabir Bichi, ya dauki alkawarin biyawa daliban karamar hukumar Bichi da su ka fadi kwalafayin  kudin jarabawar NECO, domin ba su damar cigaba da karatu.

Mai temaka masa kan harkokin yada labaran zamani Abdullahi Salisu Maisudan, shi ne ya tabbatar da haka, a wata ganawa da wakilin HAGO RADIO Kabiru Inuwa, Inda ya ce tuni an kammala karbar takardun daliban, a gobe Laraba za a biya kudaden ga hukumar da abin ya shafa.

Maisudan, ya kara da cewa, akwai bukatar daliban da za su ci gajiyar temakon su dage wajen karatu, domin su ma a nan gaba su zamo masu temakon  masu tasowa. Ya kuma godewa Eng. Abubakar Kabir, inda ya ce ya zama ruwan wanke matsalolin mutanen Bichi yara da manya.

Leave a Reply