EFCC ta damke dangin tsohon shugaban kasa Good Luck

29
TSOHON SHUGABAN KASA GOOD LUCK
TSOHON SHUGABAN KASA GOOD LUCK
TSOHON SHUGABAN KASA GOOD LUCK
TSOHON SHUGABAN KASA GOOD LUCK

Hukumar yaki da cin hanci ta kasa EFCC, tare da hadin gwiwar jami’an shige da fice ta kasa, ta samu nasarar cafke  Esther Oba, wadda ‘yar uwa ce ga  Mrs Patience Jonathan, matar tsohon shugaban kasar Najeriya a jiya Litinin, a  filin saukar jirage na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, jim kadan da dawowar ta daga birnin Dubai tare da iyalanta.

Rahotanni da su ka iske majiyar Hago Radio sun ce, ana tuhumar Esther Oba,  biyo bayan samun daya daga  asusun ajiya na matar tsohon shugaban kasa Patience Jonathan, wanda ke dauke da sa hannun ta, yayin da asusun ya kasance  makare da kudi har zambar N317,397,458.26. wato miliyan dari uku da sha bakwai, da dubu dari uku da casa’in da bakwai, da naira dari hudu da hamsin da takwas, da kwabo ashirin da shida.

Leave a Reply