Daurin auren ‘yar gidan gwamna Ganduje, da dan gwamnan Oyo ya janyo cacar baki

81
FATIMA GANDUJE DA IDRIS AJIMOBI
FATIMA GANDUJE DA IDRIS AJIMOBI
FATIMA GANDUJE DA IDRIS AJIMOBI
FATIMA GANDUJE DA IDRIS AJIMOBI

 A yau Asabar 3-3-2018 aka daura auren ‘yar gidan gwamnan jahar Kano  Fatima Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da dan gidan gwamnan jahar Oyo Idris Abolaji Abiola Ajimobi,  wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari, da Bola Tinubu su ka kasance iyayen ango da amarya

Yayin daurin auren an ga matemakin shugaban kasa, da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, da gwamnoni kimanin guda 25, da sauran sanatoci da ministoci da ‘yan majalisar tarayya na jahohi da dama. Sai dai yanzu haka wancan daurin aure ya janyo rigima ta musayar maganganu, kan yadda aka gaza ganin sanatan Kano ta tsakiya  Rabi’u Musa Kwankwaso.

Ibrahim Musa, wanda ya ke dan Gandujiya, ya ce yayi mamakin kin zuwan Sanata Kwankwaso.

” Gaskiya na yi mamaki, kan yadda manyan mutane su ka zo wajen wannan daurin aure, amma abin kunya aikin musulunci Kwankwaso ya ki zuwa”

Amma daga tsagin ‘yan Kwankwasiyyar, Usaini Muktar ‘Yarkanya, ya ce bai yi mamakin kin zuwan Kwankwaso ba, domin ba a gayyace shi ba,

” Ba a gayyaci Kwankwaso ba, to mai zo ya yi?  bayan kuma musulunci ya hana  zuwa gayyar sodi?

 

Leave a Reply