Dan majalisar tarayya Hon. Jobe ya amince da Buhari 2019

55
HON TIJJANI ABDULKADIR JOBE
HON TIJJANI ABDULKADIR JOOBE

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin Tofa Rimingado da Tofa daga jahar Kano Hon Tijani Abdulkadir  Jobe, ya ce yana goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake fitowa takara a shekara ta 2019, domin cigaba da samar da ayyukan raya  kasa da inganta tsaro da kuma farfado da tattalin araziki.

Dan majalisar, ya fadi haka ne a wata ganawa da wakilin HagoRadio ta wayar Selula, inda ya ce ya zama wajibi al’ummar Najeriya su jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari ” Gaskiya danjarida, ina so in tabbatar maka cewa, ina goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin cigaba da inganta kasa, domin kafin zuwan sa, akwai Jahohi da yawa ba sa iya biyan albashi amma yanzu waccan matsala ta zama tarihi, saboda haka ina kira ga mutanen Najeriya su sake marawa Buhari, domin shi ne maganin matsalalolin Najeriya”

Hon. Tijani Abdulkadir Jobe, ya kuma godewa al’ummar mazabunsa bisa yaddasu ka ara masa lokaci har karo uku a matsayin wakilinsu ” Ina sake amfani da wannan dama domin jinjinawa mutanen mazabu na Dawakin Tofa Rimingado da Tofa, hakika sai godiya domin sau uku su ka zabo ni a matsayin wakili, donhaka, ina ba su tabbacin cewa ina tare da su a kowanne lokaci da yardar Allah zan ci gaba da bijiro da ayyukan raya kasa.

Leave a Reply