Dan majalisar Jibiya Hon Mustafa Yusif, ya debi ‘yan kallo a mazabarsa

10
Hon Mustafa Yusif
Hon Mustafa Yusif
Hon Mustafa Yusif
Hon Mustafa Yusif

Dan majalisar jaha mai wakiltar karamar hukumar Jibiya, a zauren majalisar Katsina, Hon Mustafa Yusif, ya samu yabo ta bakin jama’arsa, kan ayyukan raya kasa da ya samar, wanda a cewarsu, shekaru da dama ba su taba samun jagaora kamar sa ba.

Daya daga al’ummar yankin Bishir Umar, shi ne ya fadi haka a wata ganawa da wakilin Hago Radio na Katsina, Abdullahi Garba Jani, inda ya ce, kasancewar Mustafa, a matsayin jagora a majalisar Katsina, ya fito da abin boye fili, domin a jagorancin baya ba a yi musu aiki.

” Bashakka Hon Mustafa Yusif, ya zama abin yabo da jinjina, domin zuwansa majalisar dokokin Katsina, mun samu abubuwan cigaba, kama daga wanda ya samar da kudinsa, da kuma wanda ya kai kudiri aka kawo, misali, samar da Taransifomomi, a garin Jibiya, Magama,Kusa Gidan Ruwa, samar da magudanar ruwa a garin Jibiya, gyaran wutar lantarki a garin Faru, Lankwasau, Daga, Riko, Tankuri, Gangara, samar da tsaro a garin Shinfida da Kewaye, da garin Jibiya, da gyaran makarantun Firamare da Sakandire, tallafin kudin sana’a  ga mata masu marayu, da sauransu”

Bashir, ya kara da cewa duba da wadannan ayyukan raya kasa, ya zama wajibi su ci gaba da goya masa baya.

 

 

Leave a Reply