Dalibai 200 sun ci gajiyar tallafin NECO daga Eng, Abubakar Kabir Bichi

21
Eng Abubakar Kabir Bichi
Eng Abubakar Kabir Bichi
Eng Abubakar Kabir Bichi
Eng Abubakar Kabir Bichi

Shugaban kamfanin gine-gine na BICO Construction Nig Limited, Eng. Abubakar Kabir Bichi, ya gwangwaje wasu daga cikin dalibai karamar hukumar Bichi, su dari biyu  da kudade domin biyan jarabawar NECO.

Cikin jawabin mai temaka masa kan harkokin yada labaran zamani Abdullahi Maisudan, ya ce, taimakon ya zama wajibi duba da yadda daliban su ka hadu da matsalar jarabawar, wanda yanayin rashin kudi da ake fama iyaye da yawa ba za su iya daukar nauyin yaransu ba, musamman duba da yanayin da ake ciki,, sabodahaka, Eng. Abubakar Kabir Bichi, ya bayar da wannan agaji.

Salihi Idiris, shi ne jagoran da ya wakilci Eng. Abubakar wajen m daikawa makarantun kudaden jarabawar, makarantun dai sun hada,  GSS DANZABUWA, GGASS DANZABUWA GSS CHIROMAWA, GSS BUDEN GARI GGSS BICHI GGASS SABON LAYI.

Daliban da su ka amafana sun yi godiya da wannan tallafi.

Leave a Reply