Da alama shugaban kasa Buhari zai sake takara 2019

66
SANATA ABU IBRAHIM
SANATA ABU IBRAHIM
SANATA ABU IBRAHIM

Kungiyar magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, karkashin jagorancin sanata Abu Ibrahim, sun nemi ya  amsa kiran ‘yan Najeriya don sake yin takarar shugabancin kasa a shekara ta 2019.

Sanatan, ya yi wannan roko  lokacin da ya ke ganawa da manema labarai  a fadar mulkin Villa,wakilin Hago Radio, ya rawaito cewa, lokacin da manema labarai ke tambayarsa ko su na da bukatar Buhari ya sake yin takara, nan take ya amsa da cewa kwarai.

“Kwarai, na goyi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake tsayawa takarar shugabancin kasa, domin mun gamsu cewa jagora ne mai kishin kasa, ya kuma cika alkawuran da ya daukarwa ‘yan Najeriya”

Yanzu abin jira a gani shin, wannan bukata za ta samu karbuwa wajen shugaban kasar, ya kuma ‘yan Najeriya za su karbi abin.

Leave a Reply